Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya bayyana goyon bayansa ga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da kuma ƙungiyar siyasa ta Rainbow Coalition ƙarƙashin jagorancin Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Fubara ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin bikin aza harsashin sake gina da kuma samar da kayan aiki ga cibiyar Riven Medical Facility, wani shiri na haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu.
A cewarsa, rikicin siyasar da ya daɗe yana addabar Jihar Ribas ya zo ƙarshe, tare da yin kira ga magoya bayansa da su mara wa dukkan 'yan takarar Rainbow Coalition baya.
Gwamnan ya ce, "Ina goyon bayan Rainbow Coalition. Shugaba Bola Ahmed Tinubu shi ne shugabanmu kuma shi muke goyon baya. Haka kuma, ɗan takarar gwamna shi ne ɗan takarar da nake goyon baya, kuma duk wanda ya yi imani da ni ya goyi bayan dukkan 'yan takarar Rainbow Coalition."
Kalaman na Fubara na zuwa ne yayin da shirye-shiryen siyasa ke ƙara ƙamari gabanin zaɓen shekarar 2027.