Magajin Garin New York ya bayyana cewa akwai dalilan da suka sa Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) ta ayyana Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, a matsayin wanda ake tuhuma da aikata laifuffukan yaƙi.
Ya ce yana goyon bayan matakin kotun na gurfanar da Netanyahu tare da gudanar da shari'a kamar yadda ake yi wa duk wanda ICC ke tuhuma.
Sai dai ya bayyana cewa hukumomin Birnin New York ba su da ikon aiwatar da sammacin kama da ICC ta fitar, saboda dokokin Amurka. Duk da haka, ya yi kira ga gwamnatin tarayyar Amurka da ta haɗa kai da kotun wajen aiwatar da umarnin.
Magajin Garin ya kuma ce ba sa maraba da Netanyahu a Birnin New York, haka kuma da duk wani mutum da Kotun ICC ke nema ruwa a jallo.
Kalaman nasa sun zo ne kwana guda bayan Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa babu wanda zai kama Netanyahu a cikin Amurka.
Ana sa ran Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, zai ziyarci birnin New York a watan Satumba domin halartar zaman Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya.