Rahotanni daga Italiya na cewa Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta ƙasar (FIGC) ta fara tattaunawa da tsohon kocin Manchester City, Pep Guardiola, domin yiwuwar naɗa shi a matsayin sabon mai horas da tawagar ƙasar.
Bayanan sun ce sabon Daraktan Fasaha na FIGC, Paolo Maldini, tare da mai ba shi shawara, Leonardo, sun yi tafiya zuwa birnin Barcelona inda suka shafe kwanaki uku suna ganawa da Guardiola kan yiwuwar karɓar aikin.
Rahotannin sun kuma ce tsoffin 'yan wasan Italiya, Roberto Mancini da Andrea Pirlo, na cikin waɗanda ake la'akari da su domin wannan muƙami.
Idan Guardiola ya amince da aikin, zai zama mutum na biyu da ba ɗan ƙasar Italiya ba da zai jagoranci tawagar ƙasar, kuma na farko tun daga shekarun 1960.
Ko da yake bai taɓa horas da wata ƙungiya a Italiya ba, Guardiola ya san ƙwallon ƙasar sosai, kuma ya taɓa taka leda a gasar Serie A tsakanin shekarun 2001 da 2003, inda ya buga wa ƙungiyoyin Brescia da Roma wasa.
Tawagar Italiya ta lashe gasar cin Kofin Nahiyar Turai (EURO) a shekarar 2021, amma daga baya ta kasa samun gurbin shiga gasar cin Kofin Duniya sau uku a jere.
Rahotanni sun ce ana neman sabon koci ne bayan Gennaro Gattuso ya bar muƙaminsa a watan Afrilu. Sai dai har yanzu Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Italiya ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan wanda za ta naɗa a matsayin sabon kocin tawagar ba.