Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ƙaddamar da kashi na biyu na shirin takardun lamuni na naira biliyan 729 domin biyan basussukan da ake bin fannin wutar lantarki da kuma inganta samar da lantarki a faɗin ƙasar.

Ministan Kuɗi kuma Ministan Kula da Tattalin Arziki, Taiwo Oyedele, ne ya sanar da hakan yayin wani taron masu zuba jari da aka gudanar a Abuja.

A cewarsa, sabon shirin ya biyo bayan kashi na farko na takardun lamuni na naira biliyan 520, wanda ya ce an saye gaba ɗaya kuma an fara amfani da kuɗaɗensa wajen biyan basussukan da aka tanada.

Ministan ya bayyana cewa shirin na daga cikin matakan gwamnatin tarayya na rage basussukan da ke addabar fannin wutar lantarki, inda za a yi amfani da kuɗaɗen wajen biyan basussukan da aka tantance na kamfanonin samar da wutar lantarki da masu samar da iskar gas.

Ya ce matakin zai taimaka wajen inganta harkokin kuɗi a fannin, ƙara yawan wutar lantarki da ake samarwa, tare da ƙarfafa amincewar masu zuba jari.

Taiwo Oyedele ya kuma ce tattalin arzikin Najeriya ya samu bunƙasar kashi 3.9 cikin 100 a rubu'in farko na shekarar 2026, yana mai cewa gyare-gyaren da gwamnati ke aiwatarwa na ci gaba da haifar da sakamako mai kyau.

Ministan ya yi kira ga masu zuba jari da su ci gaba da haɗa kai da gwamnati wajen bunƙasa tattalin arziki da kuma jawo ƙarin zuba jari mai ɗorewa a ƙasar.