Ministan tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta samu maki 70 cikin 100 kan kokarin da
take yi wajen magance matsalar tsaro a kasar nan.
Christopher Musa ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na ARISE, domin nazarin shekaru uku da gwamnatin
Tinubu ta yi tana mulki, kamar yadda jaridar Punch ta rawaito.
A cewarsa, duk da cewa har yanzu ana
fama da wasu matsalolin sace mutane da hare-haren 'yan bindiga, amma matakin ta'addanci a Nijeriya ya ragu sosai idan aka kwatanta da shekarun baya.
Ministan ya ce babu wata kasa a duniya da ta kubuta gaba daya daga matsalolin ta'addanci, yana mai cewa hare-haren da ake gani yanzu sun samo asali ne daga lalacewar tarbiyya da tsarin iyali