A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, rundunar ta miƙa godiyarta ga gwamnatin jihar Kano bisa goyon baya da haɗin kai da ta bayar ga jami’an tsaro a lokacin bukukuwan Sallah.
Sanarwar ta kuma yaba wa sarakunan gargajiya a faɗin jihar bisa irin gudunmawar da suka bayar wajen tabbatar da zaman lafiya da bin doka da oda.
Rundunar ta jinjinawa al’ummar jihar Kano saboda addu’o’i, goyon baya da kuma bin shawarwarin tsaro da aka bayar, tana mai cewa hakan ya nuna haɗin kai da jajircewar jama’ar jihar wajen tabbatar da zaman lafiya.
Haka kuma, rundunar ta yaba wa haɗaɗɗun jami’an tsaro da suka yi aiki a lokacin Sallah bisa sadaukarwa da ƙwazon da suka nuna wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma tare da hana afkuwar wata matsala ta tsaro.
Kwamishinan ’Yan Sandan jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya tabbatar wa jama’a cewa rundunar za ta ci gaba da ɗaukar matakan tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar.
Ya kuma buƙaci mazauna jihar da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro haɗin kai tare da gaggauta kai rahoton duk wani abu da ke haifar da zargi ta lambobin gaggawa na rundunar.