Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya ce gwamnatinsa ta shimfiɗa tubalin magance matsalolin da suka daɗe suna addabar ƙasar, duk da cewa har yanzu ba a kai ga cimma dukkan manufofin da aka sa gaba ba.

A jawabinsa na cikar shekara uku a mulki, Tinubu ya bayyana cewa ya fahimci irin ƙalubale da sadaukarwar da iyalai suka fuskanta a cikin shekarun baya-bayan nan, tare da nuna ƙwarin gwiwar cewa Najeriya na kan hanyar samun ci gaba.

Shugaban ya jaddada cewa harkar tsaro na daga cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa ta fi bai wa muhimmanci, yana mai cewa ana ci gaba da samun nasarori duk da ƙalubalen da ake fuskanta.

Ya kuma tabbatar wa ƴan Najeriya cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiki domin tabbatar da zaman lafiya da samar da yanayin da jama’a za su gudanar da harkokinsu ba tare da tsoro ko fargaba ba.

Tinubu ya ce babban aikin da ke gaban gwamnati yanzu shi ne tabbatar da cewa al’umma sun fara amfana kai tsaye daga sauye-sauyen tattalin arziƙin da ake aiwatarwa.

Haka kuma ya ce gwamnati na ƙoƙarin tabbatar da cewa farashin kayayyakin masarufi da ya fara sauka tun daga shekarar 2023 zuwa 2024 bai sake tashin gwauron zabi ba.

Shugaban ya ƙara da cewa gwamnati na aiki kan rage kuɗin sufuri ta hanyar ƙarfafa amfani da motocin gas da na lantarki a faɗin ƙasar.