Jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo a matsayin ɗan takarar gwamnan jam’iyyar NDC a zaɓen shekarar 2027.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya kuma sanar da cewa Dakta Nasiru Yusuf Gawuna zai nemi kujerar Sanatan Kano ta Tsakiya.
Ya ce an ɗauki matakin ne bisa la’akari da gaskiya, biyayya da ƙwarewa, waɗanda ya bayyana a matsayin ginshiƙan haɗin kai da ci gaban Kwankwasiyya.
Sanarwar na zuwa ne bayan kwanaki ana gudanar da tattaunawa tsakanin mambobin Kwankwasiyya da wasu manyan ƴan siyasa kan shirye-shiryen zaɓen 2027.
Aminu Abdussalam Gwarzo ya sauka daga muƙaminsa na mataimakin gwamnan Kano a watan Maris bayan rikicin siyasa da ya biyo bayan ficewar gwamna Abba Kabir Yusuf daga jam’iyyar NNPP zuwa APC.