Gwamnatin Tarayyar Najeriya na duba yiwuwar kakaba takunkumin tafiye-tafiye kan jiragen da ke fitowa daga ƙasashen da ke fama da cutar Ebola, a wani ɓangare na sabbin matakan kare ƙasar daga yaduwar cutar.

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila ne ya bayyana hakan yayin wani taro na musamman da aka gudanar a Legas domin nazari kan shirin Najeriya na tunkarar Ebola.

Ya ce ana kuma nazarin yiwuwar maye gurbin takunkumin tafiye-tafiye da tsarin keɓe fasinjojin da ke nuna alamun kamuwa da cutar.

Taron ya samu halartar manyan jami’ai da suka haɗa da Darakta Janar na NCDC, Jide Idris, Ministan Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, da Kwamishinan Lafiya na Jihar Legas, Akin Abayomi.

Gbajabiamila ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya riga ya samu cikakken bayani kan halin da ake ciki a Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo da Uganda, inda ya tabbatar da cewa gwamnati za ta ɗauki matakan da suka dace domin hana shigowar cutar Najeriya.