Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi na Jihar Kano, Dakta Dahir M. Hashim, ya yaba wa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa abin da ya bayyana a matsayin nuna kwarewa, gogewa da hikima wajen tafiyar da batun fitar da ƴan takarar jam’iyyar APC a jihar.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, Dakta Dahir Hashim ya taya gwamnan murnar nasarar gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar cikin lumana a fadin jihar Kano, yana mai cewa tsarin ya gudana cikin natsuwa da fahimtar juna tsakanin masu ruwa da tsaki.
Ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna ƙwarewar siyasa ta hanyar haɗa kan mambobin jam’iyyar da tabbatar da cewa muradun jam’iyya sun fi fifikon buƙatun kai.
A cewarsa, yadda aka gudanar da zaben cikin tsari da zaman lafiya alama ce ta shugabanci nagari da kuma yadda ake ci gaba da samun amincewar jama’a kan jagorancin gwamnan.
Dakta Dahir ya ƙara da cewa nasarar zaben fidda gwanin ba kawai kammala wani mataki na siyasa ba ne, illa wata muhimmiyar nasara ce wajen ƙara ƙarfafa jam’iyyar gabanin zabukan da ke tafe.
Ya bayyana Gwamna Abba Kabir Yusuf a matsayin jagora mai tafiya cikin natsuwa da hikima, wanda ke iya haɗa kan jama’a tare da samar da sakamako mai amfani ga jam’iyya da al’umma baki ɗaya.
Haka kuma ya ce haɗin kai da tsarin da aka nuna yayin gudanar da zaben ya ƙara tabbatar da cewa jam’iyyar APC na da ƙarfin ci gaba da samar da shugabanci nagari da ci gaba mai dorewa, duk da ƙalubalen da ake fuskanta.
A ƙarshe, ya sake taya gwamnan murna, yana mai cewa abin da aka samu ya zama babban misali na shugabanci mai hangen nesa da kishin ci gaban al’umma.
Dakta Dahir M. Hashim shi ne Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi na Jihar Kano, kuma mukaddashin Kwamishinan Ma’aikatar Albarkatun Ruwa.