Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana Bimbo Adekanmbi a matsayin wanda yake fatan zai gaje shi a kujerar gwamnan jihar a zaben shekarar 2027.
Makinde ya bayyana hakan ne yayin taron gangamin haɗin gwiwa na jam’iyyun PDP da APM da aka gudanar a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, inda aka kuma kaddamar da Adekanmbi a matsayin ɗan takarar gwamna na bai ɗaya na jam’iyyar APM.
Gwamnan ya ce al’ummar jihar Oyo sun amfana da tsare-tsaren gwamnatinsa na “Omituntun 1.0” da “Omituntun 2.0”, yana mai bayyana cewa yanzu lokaci ya yi na aiwatar da “Omituntun 3.0”.
Haka kuma, Makinde ya shawarci Adekanmbi da kada ya yi koyi da makiyansa, sai dai ya samar da nasa salon shugabanci tare da ci gaba da ayyukan ci gaba da gwamnatinsa ta fara, domin amfanin al’ummar jihar baki ɗaya.