Ana zargin wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon Daraktan Yaɗa Labarai na Rundunar Sojin Najeriya, Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya, tare da matarsa a Jihar Katsina.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar a yankin Matazu lokacin da tsohon jami'in sojan da matarsa ke kan hanyarsu ta zuwa birnin Katsina.
Maharan sun tare motar da suke ciki tare da yin awon gaba da su zuwa wani wuri da ba a bayyana ba.
Wata majiya ta tsaro ta bayyana cewa direban motar ya samu raunukan harbin bindiga yayin harin, amma ya samu nasarar tserewa daga hannun maharan.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Rundunar 'Yan Sandan Jihar Katsina da Rundunar Sojin Najeriya ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan faruwar lamarin ba.