Wani ɗan majalisar dokokin Iran, Jafar Pourkabagani, ya bayyana cewa ƙasar ta yi asarar da ta kai kusan dala biliyan huɗu a filin gas na South Pars sakamakon hare-haren da suka afku yayin rikicin baya-bayan nan.

A cewarsa, wannan ƙiyasin ya samo asali ne daga binciken haɗin gwiwa da ƙwararru da masana daga Jami’ar Kimiyya da Fasaha suka gudanar. Ya ƙara da cewa raguwar ayyukan da aka samu a filin na haifar da asarar kusan dala miliyan biyu a kowace rana.

Rahotanni sun nuna cewa a lokacin rikicin, Amurka da Isra’ila sun kai hare-hare kan wasu wurare a filin South Pars, wanda ake ɗauka a matsayin mafi girman filin iskar gas a duniya da ke cikin Tekun Fasha.

Filin na da muhimmanci matuƙa ga ɓangaren makamashi, kasancewar Iran da Qatar ne ke raba mallakarsa. Iran na sarrafa ɓangaren da ake kira South Pars, yayin da Qatar ke kula da ɓangaren arewa na filin.

Qatar na daga cikin manyan ƙasashen da ke fitar da iskar gas a duniya, inda take samar da kusan kashi 20 cikin 100 na iskar gas da ake amfani da ita a kasuwannin duniya. Saboda haka, duk wani tangarda da ya shafi filin na iya yin tasiri ga wadatar makamashi a duniya.

A wani ɓangaren kuma, wakilin yankunan Bushehr, Genaveh da Daylam ya bayyana cewa an kai hare-hare sau uku kan Cibiyar Kula da Yanayi ta Bushehr, lamarin da ya janyo lalacewar wasu sassan cibiyar.

Ya kuma ce filin jirgin saman Bushehr na ci gaba da kasancewa cikin yanayi mai kyau ta fuskar kayan aiki, amma sake buɗe shi ga zirga-zirgar jirage zai dogara ne da amincewar hukumomin tsaro bayan kammala tantance halin da ake ciki.