Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) kuma Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bayyana cewa gwamnoni na duba yiwuwar ƙara mafi ƙarancin albashin ƙasa zuwa Naira 100,000.
A cewar rahoton da jaridar Punch ta wallafa, AbdulRazaq ya bayyana hakan ne ta cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya danganta matakin da hauhawar farashi, tsadar rayuwa da kuma matsin tattalin arziƙin da ma’aikata ke fuskanta.
Ya ce gwamnatocin jihohi na ci gaba da tattaunawa da gwamnatin tarayya da kuma ƙungiyoyin ƙwadago domin samar da matsaya kan sabon tsarin albashi wanda zai taimaka wajen inganta walwalar ma’aikata tare da la’akari da ƙarfin jihohi wajen biyan albashin.
AbdulRazaq ya bayyana cewa manufar shirin ita ce ƙara ƙarfin sayen kayan masarufi na ma’aikata, tare da tabbatar da cewa gwamnatoci na da damar ci gaba da gudanar da ayyukan raya ƙasa da samar da muhimman ayyukan jama'a.
A halin yanzu, mafi ƙarancin albashi a Najeriya na tsaye a kan Naira 70,000 a wata, duk da cewa wasu jihohi sun riga sun fara biyan albashin da ya zarce wannan adadi.