Dan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar NDC kuma tsohon mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya soki Gwamna Abba Kabir Yusuf, inda ya zarge shi da yin sakaci wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.
A wata hira da ya yi da BBC Hausa, Kwamared Aminu Abdussalam ya bayyana cewa yanayin tsaro a Kano ya taɓarɓare fiye da kowane lokaci a tarihin baya-bayan nan.
Ya ce a wasu ƙananan hukumomi irin su Tsanyawa, Shanono da Gwarzo, an samu hare-hare da suka yi sanadin kisan mutane da kuma kwashe dukiyoyi. Ya kuma yi zargin cewa har yanzu akwai wasu da ke tsare sama da watanni shida sakamakon rikice-rikicen tsaro.
A cewarsa, hatta a cikin birnin Kano ma ana ci gaba da samun kashe-kashe, inda ya ce cikin makonni uku kaɗai an rasa rayuka da dama, lamarin da ya ce ya jefa jama’a cikin fargaba da tashin hankali.
Ya kuma ce ranar rantsar da mataimakin gwamna ma an samu rahoton mutuwar mutane biyar, abin da ya ce ya nuna irin matsin da ake ciki a fannin tsaro.
Aminu Abdussalam ya ƙara da cewa taken “Kano First” da gwamnatin jihar ta bullo da shi bai haifar da zaman lafiya ba, a maimakon haka ya ce ya zo da sabanin abin da aka yi alkawari.
Ya kuma bayyana cewa taken da aka kwafa daga “America First” bai dace da al’adar siyasar Najeriya ba, yana mai cewa abin da ya kamata shi ne haɗin kai da tsari mai inganci wajen magance matsalar tsaro.
A cewarsa, gwamnan da kansa ya taɓa bayyana cewa “Kano First” za ta kawo zaman lafiya, sai dai ya zarge shi da cewa abin ya zama sabanin haka a aikace.