Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya tabbatar wa 'yan Najeriya cewa gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro za su ci gaba da yin duk mai yiwuwa domin ganin an ceto mutanen da aka yi garkuwa da su a sassan kasar nan.

‎Musa ya bayyana hakan ne jiya Asabar bayan da aka karrama shi da lambar yabo ta Southern Kaduna Grand Commander a wajen bikin al'adun Kudancin Kaduna na shekarar 2026.

‎Ya amince cewa har yanzu akwai wasu mutane da ke hannun masu garkuwa da mutane, yana mai jaddada cewa jami'an tsaro ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da an kubutar da su.

‎Ministan ya ce hadin kai tsakanin al'umma da hukumomin tsaro na da matukar muhimmanci wajen yaki da matsalar rashin tsaro da kuma tabbatar da dawo da wadanda aka sace.