Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta aiwatar da kusan kashi 90 cikin 100 na alƙawuran da ta ɗauka wa al’ummar jihar tun bayan hawanta mulki.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi bakuncin Sarkin Rano, Ambasada Muhammad Isa Umaru, wanda ya kai masa ziyarar Sallah a Fadar Gwamnatin Kano ranar Asabar.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, Gwamna Yusuf ya ce gwamnatinsa ta mayar da hankali wajen aiwatar da shirye-shiryen ci gaba da manufofin da suka shafi rayuwar jama'a kai tsaye.
Ya ce an samu gagarumin ci gaba a fannoni da suka haɗa da ilimi, lafiya, ababen more rayuwa, noma, samar da ruwa, ƙarfafa matasa da kuma bunƙasa tattalin arziki, waɗanda a cewarsa ke da nufin inganta rayuwar al’umma da tabbatar da ci gaban jihar mai ɗorewa.
A nasa jawabin, Sarkin Rano ya yaba wa gwamnan kan abin da ya bayyana a matsayin manyan nasarorin da aka samu cikin shekaru uku na mulkinsa.
Ya ambaci kammala ayyukan hanyoyi masu tsawon kilomita biyar a ƙananan hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure, da kuma ci gaban da aka samu a aikin samar da ruwan Kaluwaiwai a matsayin wasu daga cikin nasarorin gwamnatin.
Hakazalika, Sarkin ya jinjinawa gwamnatin jihar kan rawar da ta taka wajen ɗaukaka Asibitin Rano zuwa Babban Asibitin Tarayya (FMC), da kuma mayar da Makarantar Fasahar Karkara ta Rano zuwa Kwalejin Fasaha ta Tarayya.
Ya kuma tabbatar da ci gaba da goyon bayan Masarautar Rano ga gwamnatin jihar domin tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba a Kano da Najeriya baki ɗaya.