Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya amince tare da bada umarnin baza jami'an tsaron gandun daji guda 1,000 domin ceto dalibai da malamai da aka yi garkuwa da su a jihar Oyo
Wannan na cikin wata sanarwa da mai bai wa Shugaban Shawara kan yaɗa labarai Bayo Onanuga ya fitar.
Onanuga yace wata babbar tawaga ta gwamnatin tarayya ta isar da umarnin Shugaban ga shugabannin al’umma da ‘yan majalisu yayin wata ziyara da ta kai ƙauyukan Esiele da Yawota da ke ƙaramar hukumar Oriire a ranar 31 ga Mayu, 2026.