Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya musanta rahotannin da ke cewa zai fice daga jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM) domin zama mataimakin tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, a zaɓen 2027 ƙarƙashin wani ɓangaren PDP.
Mohammed ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya ce hankalinsa yana kan neman kujerar Sanatan Bauchi ta Kudu a ƙarƙashin jam’iyyar APM a zaɓen 2027.
Ya buƙaci jama’a da su yi watsi da duk wasu rahotannin da ke nuna yana da wata manufa ta siyasa daban, yana mai cewa irin waɗannan rahotanni hasashe ne marasa tushe.
Rahotannin sun biyo bayan sanar da Jonathan a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na wani ɓangaren PDP ƙarƙashin jagorancin Kabiru Turaki domin zaɓen 2027.
A kwanakin baya ne Bala Mohammed ya fice daga PDP tare da komawa APM sakamakon rikicin da ke addabar jam’iyyar adawa.