Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alhininsa ga iyalan dalibai da malamai da aka sace a karamar hukumar Oriire ta jihar Oyo, yana mai cewa babu wani yaro da ya kamata a dauke shi daga cikin aminci da kariyar da makaranta ke bayarwa.
A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Litinin, shugaban kasar ya ce yana tare da iyalan wadanda abin ya shafa cikin wannan lokaci na damuwa da tashin hankali bayan harin da aka kai garuruwan Esiele da Yawota.
Tinubu ya ce babu wani yaro da ya kamata a sace shi daga aji, kuma babu wani uba ko uwa da ya kamata ya shiga irin wannan azaba da damuwa.
Shugaban kasar ya kuma mika ta’aziyyarsa ga iyalan malamin da aka kashe yayin harin, Michael Oyedokun, wanda aka ce masu garkuwa da mutane sun kashe shi.
Ya ce sadaukarwar marigayin ba za ta taba mantuwa ba, kuma gwamnati ba za ta yi watsi da iyalansa ba.
Tinubu ya tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da gudanar da ayyukan ceto cikin hikima da hadin gwiwa, tare da amfani da hanyoyin tsaro daban-daban domin tabbatar da dawowar dalibai da malamai gida lafiya.
Ya ce za a yi amfani da duk wata hanya da doka ta amince da ita, ta fuskar tsaro da tattaunawa, domin ganin an kubutar da wadanda aka sace.
Wannan sanarwa ta biyo bayan ziyarar wata babbar tawagar gwamnatin tarayya da aka tura yankunan da abin ya shafa bayan harin da ya faru ranar 15 ga Mayu, 2026.
Tawagar ta kunshi manyan jami’an gwamnati da tsaro ciki har da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila; Mai Bai Wa Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaro, Nuhu Ribadu; Ministan Tsaro; da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun.
Shugaban kasar ya kuma sake jaddada matakan tsaro da aka dauka a yankin, ciki har da tura runduna ta musamman da ke da kwarewar gudanar da ayyukan ceto.
Haka kuma ya ce gwamnatin tarayya tare da gwamnatin jihar Oyo za su dauki masu gadin dazuka 1,000 domin kara tsaro da sanya ido a yankunan da masu aikata laifuka ke amfani da su.
Tinubu ya kara da cewa ya bayar da umarnin a tura rundunar musamman mai kayan aiki na zamani domin kara kaimi wajen kubutar da dalibai da malamai da aka sace.
Ya kuma bayyana cewa bukatar kafa sansanin soji a yankin na samun kulawa ta musamman daga gwamnati.
Lamarin sace dalibai da malamai a garuruwan Esiele da Yawota ya kara tayar da hankalin jama'a kan matsalar tsaron makarantu da kuma rashin tsaro a yankunan karkara, yayin da jami'an tsaro ke ci gaba da kokarin ganin an kubutar da wadanda aka sace tare da kara tsaro a yankunan da ke cikin hadari.