Kwamishinan Lafiya na jihar, Farfesa Akin Abayomi, ya jagoranci wata tawaga ta musamman domin duba shirye-shiryen kariya a Filin Jirgin Sama na Murtala Mohammed da ke Legas.
Matakin ya biyo bayan rahotannin sake ɓarkewar cutar Ebola a ƙasashen Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo da Uganda.
Yayin ziyarar, tawagar ta tantance tsarin kula da fasinjoji, hanyoyin dakile yaduwar cututtuka, shirye-shiryen gaggawa da kuma matakan haɗin gwiwa tsakanin hukumomin lafiya da na filayen jiragen sama.
Farfesa Abayomi ya bayyana cewa Filin Jirgin Sama na Murtala Mohammed shi ne mafi muhimmancin ƙofar shiga Najeriya, domin kusan kashi 70 cikin 100 na matafiya daga ƙasashen waje suna bi ta cikinsa. Ya ce gwamnati na ƙoƙarin ƙarfafa hanyoyin gano masu alamun cutar da wuri, killace su cikin gaggawa da kuma sa ido kan matafiya daga ƙasashen da ake fargabar cutar