Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya bukaci ’yan Najeriya su rika yin gwaje-gwajen lafiya akai-akai domin gano cututtuka tun da wuri tare da samun damar kula da su yadda ya kamata. 


Ya ce hakan na da matukar muhimmanci musamman wajen yaki da cututtuka kamar su kansa da ciwon sukari.


Obasanjo ya bayyana hakan ne a birnin Abeokuta yayin kaddamar da wani shiri da aka shirya domin wayar da kan jama’a game da cutar kansar mafitsara.


Da yake bayar da misali daga rayuwarsa, Obasanjo ya bayyana cewa ya shafe sama da shekaru 40 yana fama da ciwon sukari amma yana sarrafa shi ta hanyar motsa jiki, kula da abinci da kuma samun isasshen hutu