Amurka ta tisa ƙeyar wasu ƴan asalin yammacin Afirka ta yamma zuwa Ghana, kamar yadda wani lauya da ke da hannu a lamarin ya shaida wa manema labaru
Shugaban Amurka Donald Trump ya ci gaba da aiwatar da tsauraran matakan hana shige da fice, ciki har da korar mutanen da galibi ake shirin ba su izinin zama a Amurka a karkashin gwamnatocin da suka gabata.
Sannan ya na amfani da wasu yarjejeniyoyin da suka baiwa ƙasar damar tura mutanen zuwa kasashen da ba su da alaka,
A shekarar da ta gabata ne dai Ghana ta karɓi baƙuncin wasu 'yan kasashen yammacin Afirka na wani dan lokaci kafin a tura su kasashensu, ciki har da mutanen da jami’an hukumar shige da fice ta Amurka suka gano kan iya fuskantar tsangwama a kasashensu na asali