Ƙungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ta ce matsalar rashin tsaro da kashe-kashen da ke faruwa a ƙasar ba ta taƙaitu ga Kiristoci kaɗai ba, domin Musulmai da Kiristoci duka na fuskantar irin wannan barazana.

Shugaban CAN na Arewa, Rabaran Joseph Hayab, ya bayyana hakan yayin da yake bayani kan matakin da ƙungiyar ta ɗauka na ayyana kwanakin jimami na ƙasa tare da kira ga gwamnati ta ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro.

Hayab ya ce ƙungiyar ta yanke shawarar ɗaukar matakin ne saboda yadda kashe-kashe da hare-haren ta'addanci suka ƙaru a sassa daban-daban na ƙasar.

"Kashe-kashen ya yi yawa, dole ne mu fito mu nemi mataki. Duk waɗanda abin ya shafa 'yan Najeriya ne, Musulmai da Kiristoci," in ji shi.

Ya ƙara da cewa matsalar tsaro ta zama barazana ga kowa ba tare da la'akari da addini, yanki ko matsayi a al'umma ba, yana mai gargadin cewa idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba, illolinta za su ci gaba da shafar dukkan 'yan ƙasar.

CAN ta ayyana ranakun jimami na ƙasa daga 12 ga Yuni, 2026, tare da ware ranar Lahadi 14 ga Yuni a matsayin "Baƙar Lahadi" domin tunawa da waɗanda suka rasa rayukansu sakamakon hare-hare da tashin hankali a Najeriya.

Hayab ya kuma yi kira ga dukkan 'yan Najeriya, ba tare da bambancin addini ba, da su haɗa kai wajen neman mafita ga matsalar rashin tsaro da ke ƙara ta'azzara a ƙasar.