Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Iran ta amince ba za ta nemi mallakar makaman nukiliya ba, yana mai bayyana cewa Mojtaba Khamenei, ɗan Jagoran Addinin Iran Ayatollah Ali Khamenei, na da rawa a tattaunawar da ke gudana tsakanin Tehran da Washington.
A wata hira da ya yi a shirin podcast mai suna “Pod Force One”, Trump ya kuma bayyana cewa ya yi tattaunawa mai zafi da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu kan hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da kaiwa a Lebanon.
Sai dai ya ce duk da rashin jituwar da suka samu kan wasu batutuwan siyasa da tsaro, har yanzu yana da kyakkyawar alaƙa da Netanyahu.
A wani rahoto da Axios ta wallafa, an ce Trump ya kira Netanyahu da “mara hankali” a wata tattaunawar waya, inda ya nuna damuwa cewa matakan da Isra’ila ke ɗauka na iya ƙara juya ra’ayin duniya a kanta.
Rahoton ya haifar da cece-kuce a Isra’ila da sauran sassan duniya, musamman saboda yadda kalaman suka fito a daidai lokacin da rikice-rikice ke ci gaba da taɓarɓarewa a yankin Gabas ta Tsakiya.