Jigo a jam'iyyar APC Abayomi Nurain Mumuni, ya kare Uwargidan Shugaban Ƙasa Oluremi Tinubu, kan suka da ake mata bayan ta shawarci 'yan Najeriya da su rungumi ƙananan sana'o'i. Yana Mai cewa an yi wa kalamanta mummunar fahimta, alhali manufarta ita ce ƙarfafa dogaro da kai ta fuskar tattalin arziki, musamman ga mata da iyalai masu ƙaramin ƙarfi.
Martaninsa ya biyo bayan suka da dama da suka taso bayan Sanata Tinubu ta shawarci 'yan Najeriya, musamman mata, da su shiga ƙananan sana'o'i kamar suya da sayar da ƙosai da gasasshen masara domin inganta rayuwarsu.
Kalaman nata sun haifar da zazzafar muhawara a kafafen sada zumunta, inda masu suka suke bayyana kalamanta a matsayin maras tausayi kuma ba su dace da halin da 'yan Najeriya ke ciki ba, musamman ganin hauhawar farashin kayayyaki, tsadar rayuwa da matsalar rashin aikin yi.
Sai dai a cikin wata sanarwa da ya fitar jiya, wadda mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Rasheed Abubakar, ya sanya wa hannu, Mumuni ya jaddada cewa shawarar Uwargidan Shugaban Ƙasar na da nufin ƙarfafa 'yan Najeriya su fara sana'o'in da ba sa buƙatar jari mai yawa.
Inda yace "Ina so in yi bayani kan kuskuren fahimtar da aka yi game da kiran da Uwargidan Shugaban Ƙasa ta yi na ƙarfafa sana'o'in gargajiya, musamman sana'ar sayar da ƙosai da kulili."
A cewarsa, 'yan Najeriya da dama da ke rayuwa cikin talauci ba sa buƙatar babban jari domin fara ƙananan sana'o'in da za su iya samar musu da ɗorewar hanyar samun kuɗin shiga.