Mai magana da yawun jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya bayyana cewa hukuncin na barazana ne ga dimokuraɗiyyar Nijeriya, yana mai cewa irin waɗannan matakai na iya rage damar jam’iyyun adawa a ƙasar.


A ranar Juma’a ne kotun ta soke hukuncin da ta yanke a baya wanda ya umarci INEC ta yi wa NDC rajista. Alkalin kotun, Mai Shari’a Isah Dashen, ya ce an yanke hukuncin farko ba tare da haɗa jam’iyyar PMP ba, wadda ta yi ikirarin mallakar tambarin da NDC ke amfani da shi.


ADC ta yi kira da a kare ‘yancin bangaren shari’a tare da kauce wa amfani da kotuna wajen raunana jam’iyyun adawa. Jam’iyyar ta ce ci gaba da rikice-rikicen shari’a kan jam’iyyun adawa na takaita sararin dimokuraɗiyya tare da ƙarfafa masu mulki.


Jam’iyyar ta kuma yi gargadin cewa, yayin da ya rage ƙasa da watanni bakwai a gudanar da babban zaɓe, duk wani mataki da zai iya rage amincewar jama’a da tsarin zaɓe ya kamata ya zama abin lura.


ADC ta bukaci jam’iyyun adawa, ƙungiyoyin fararen hula, ƙungiyoyin ƙwadago, lauyoyi, kafafen yaɗa labarai da sauran ‘yan Nijeriya su haɗa kai domin kare dimokuraɗiyyar ƙasa. Ta kuma jaddada cewa kundin tsarin mulki ya ba ‘yan ƙasa ‘yancin shiga siyasa da zaɓar shugabanni cikin ‘yanci.