Dakarun Sashe na 2 na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Operation FANSAN YAMMA da ke Arewa maso Yamma sun kashe wasu da ake zargin 'yan ta'addan Lakurawa biyu tare da ƙwace makamai da alburusai a wani samame da suka kai a yankin Sabarumawa na Jihar Kebbi.


An gudanar da wannan samame ne a ranar 27 ga Yuni bayan samun sahihan bayanan sirri cewa ƙungiyar na shirin kai hari kan al'ummar Sabarumawa.


Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Jami'in Yaɗa Labarai na Operation FANSAN YAMMA, Laftanar Kanar Aliyu Danja, ya fitar a ranar Lahadi.


Danja ya ce dakarun Bataliya ta 7 ta Rundunar Musamman ta Shugaban Hafsan Sojojin Ƙasa sun yi gaggawar isa yankin tare da kafa kwanton bauna a hanyar da ake zargin 'yan ta'addan za su bi domin dakile harin da suka shirya.