Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta sanar da cewa za a gudanar da daurin auren gata na angwaye 1,500 da amare 1,500 a ranar Juma'a 3 ga Yuli mai kamawa.

Wannan na cikin sanarwar da Kwamandan Hisbah na Karamar Hukumar Birni kuma kakakin ƙungiyar kwamandojin Hisbah na ƙananan hukumomi, Malam Hamidan Tanko, ya fitar.

Sanarwar ta ce Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, zai jagoranci taron, yayin da Babban Kwamandan Hisbah na Jihar Kano, Imam Aminu Ibrahim Daurawa, zai wakilce shi a matsayin uban angwaye.

Haka kuma, Sarkin Kano da ke Kofar Kudu, Khalifa Muhammadu Sanusi II, zai kasance uban amare.

Sanarwar ta ce za a gudanar da daurin auren ne da misalin karfe 2:00 na rana a Babban Masallacin Juma'a na Kano, inda ake gayyatar al'ummar Musulmi su halarta.