Al'ummar unguwar Maidile dake karamar hukumar Kumbotso anan Kano sun gudanar da wani gagarumin aikin tsaftace muhalli a matsayin matakin kare lafiyar jama'a da kuma rage illar ambaliyar ruwa da ke addabar yankin a duk lokacin damina.
Aikin ya samu halartar matasa, dattijai, shugabannin unguwa da kuma 'yan kwamitocin yankin, inda kowa ya ba da gudummawarsa wajen tabbatar da tsaftar muhalli da bude hanyoyin ruwa.
A yayin aikin, mahalarta sun yi aikin yaye magudanan ruwa da suka cika da shara tare da share hanyoyin da ruwa ke bi daga kan tituna zuwa manyan magudanan ruwa.
Al'ummar yankin sun kuma nuna damuwarsu kan halin da titin Layin Hamdala ke ciki, inda suka ce rashin ingantaccen titin da kuma magudanan ruwa ya sa ruwan sama ke gangarowa cikin unguwar Maidile, abin da ke haddasa ambaliya tare da lalata hanyoyi da gidajen jama'a.