Mai neman takarar kujerar majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar ƙaramar hukumar Tarauni, Hon. Isa Adamu Bashir (Isa Jaa), ya musanta ikirarin da dan majalisa mai ci, Hon. Kabiru Dahiru Sule ADS ya yi na cewa ya janye masa takara bisa maslaha.


Hon. Isa Adamu Bashir (Isa Jaa) ya bayyana cewa har zuwa wannan lokaci bai janye daga takarar ba, kuma babu wanda ya tuntube shi domin tattaunawar maslaha ko neman ya hakura da kudirinsa na tsayawa takara.


A cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce labarin da aka yaɗa wa na cewa ya janye wa Hon. Kabiru Dahiru Sule ADS ba gaskiya ba ne, yana mai cewa babu amincewarsa ga irin wannan matsaya.


“Na ga sanarwar da Hon. Kabiru Dahiru Sule ADS ya fitar inda ya ambaci sunana cikin waɗanda wai suka janye masa takara bisa maslaha. Ina sanar da al’ummar Tarauni cewa ban janye takara ba, kuma babu wanda ya tuntube ni ko ya yi wata tattaunawa da ni kan hakan,” in ji shi.


Ya kara da cewa yana nan daram cikin takarar kujerar majalisar dokokin jihar Kano domin wakiltar al’ummar Tarauni, yana mai jaddada cewa zai ci gaba da tuntubar al’umma da neman goyon bayansu.


Hon. Isa Adamu Bashir (Isa Jaa) ya kuma bukaci magoya bayansa da su kwantar da hankalinsu tare da ci gaba da ba shi goyon baya, yana mai cewa duk wani mataki da zai dauka zai kasance ne bisa gaskiya da mutunta ra’ayin jama’a.


Sai dai ya bayyana cewa yana girmama dukkan shugabannin jam’iyya da masu ruwa da tsaki a siyasar Tarauni, tare da kira ga ‘yan siyasa da su rika tabbatar da sahihancin bayanan da suke fitarwa domin kaucewa rudani a tsakanin magoya baya.