Dan gidan tsohon shugaban kasa Sani Abacha, wato Muhammad Sani Abacha, ya sha kaye a zaɓen fidda gwani na gwamna da jam’iyyar PDP ta gudanar a Kano.
Rahotanni sun bayyana cewa Muhammad Bello Dalhatu ne ya kayar da shi, inda ya zama ɗan takarar gwamna na jam’iyyar a babban zaɓen dake tafe.
Da yake bayyana sakamakon zaɓen, shugaban kwamitin gudanar da zaɓen fidda gwani na gwamna, Umar Danjani Hadejia, ya ce an gudanar da zaɓen cikin lumana tare da bin kundin tsarin mulkin jam’iyyar da kuma ƙa’idojin zaɓe.
Ya bayyana cewa Muhammad Sani Abacha ya samu ƙuri’u 749, yayin da Muhammad Bello Dalhatu ya samu ƙuri’u 2,233, wanda hakan ya ba shi nasarar lashe zaɓen.
Hadejia ya yabawa masu neman takara, wakilai, jami’an jam’iyya da hukumomin tsaro bisa tabbatar da gudanar da zaɓen cikin tsari da lumana