Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun Laraba 27 ga watan Mayu da Alhamis, 28 ga watan a matsayin ranakun hutu domin shagulgulan Babbar Sallah.
Cikin wata sanarwa da sakataren din-din na ma'aikatar cikin gida a madadin, ministan cikin gidan ƙasa, Olubunmi Tunji-Ojo, ya ce gwamnati ta bayar da hutun ne domin nuna martabawa ga miliyoyin musulman ƙasar.
Sanarwar ta ce an bayar da hutun ne domin musulmai su samu damar yin shagulgular Babbar Sallah kamar yadda sauran Musulman duniya ke gudanarwa.
Ministan ya kuma taya al'ummar musulmai na ciki da wajen ƙasar su yi amfani da muhimmin lokacin domin yi wa ƙasa addu'o'in samun zaman lafiya da ci gaba.
A ranar Laraba ne msulman duniya za su gudanar da Idin Babbar Sallah bayan tsayuwar Arfa da mahajjata za su yi a Saudiyya ranar Talata