Rundunar yansandan jihar Kano ta sanar da samun nasarar kama wasu manyan dilolin muggan kwayoyi tare da kama wasu kwayoyin da dama.

Haka kuma rundunar ta sake kama wasu mutanen na daban da ake zargin suma suna ta’ammalin da muggan kwayoyin.

Ta cikin wata sanarwa da mai Magana da yawun rundunar yansanda CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ya ce rundunar ta ci gaba sake bincike da sanya idanu kan wuraren da ta samu rahotanni ana aikata laifuka