Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta wanke tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, tare da tabbatar da cewa yana da damar tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2027.
A hukuncin da Mai Shari’a Peter Lifu ya yanke a ranar Talata, ya tabbatar da tarar Naira miliyan 20 da aka ci lauyan nan Johnmary Jideobi, wanda ya shigar da ƙarar.
Haka kuma kotun ta ƙara ɗora wa mai ƙarar tarar Naira miliyan ɗaya domin a biya Babban Lauyan Tarayya.
Mai shari’ar ya ce lauyan ba shi da hurumin shari’a na shigar da ƙarar, domin bai nuna wata asara da ya yi ba dangane da abin da yake zargin Jonathan na shirin tsayawa takarar zaɓen shekara mai zuwa.
Alƙalin ya kuma bayyana cewa wata Babbar Kotun Tarayya da ke Yenagoa da kuma Kotun Ɗaukaka Ƙara sun riga sun tabbatar da cewa Jonathan na da damar tsayawa takara, don haka shi ma dole ne ya bi hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙarar.
Daga nan sai ya bayyana ƙarar lauyan a matsayin “cin zarafin tsarin shari’a,” tare da yin watsi da ita saboda rashin muhimmanci.