Jami’an tsaro a Jihar Kebbi sun kama wasu mutane huɗu da ake zargi da damfarar maniyyatan aikin Hajjin bana.

Ana zargin mutanen da karɓar kuɗi daga hannun mutane da sunan samar musu guraben zuwa ƙasa mai tsarki.

Rahotanni sun nuna cewa ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin ya karɓi kuɗi har Naira 860,000 daga wani mutum, inda ya yi masa alƙawarin samar masa kujerun Hajji guda biyu.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kebbi, SP Bashir Usman, ya ce kamen ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da waɗanda abin ya shafa suka kai wa hukuma tare da haɗin gwiwar Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta jihar.

Rundunar ta tabbatar da cewa ana ci gaba da bincike domin gano cikakken yadda lamarin ya faru, tare da ɗaukar matakan doka kan waɗanda aka kama idan aka same su da laifi