Mai magana da yawun shugaban kasa Bayo Onanuga, ya furta hakane yayin da yake kare manufofin gwamnatin tarayya na karbar bashi, inda ya ce har yanzu Najeriya na da kima ta fuskar amincewar masu bada bashi, kuma tana iya sake samun karin rance domin daukar nauyin manyan ayyukan more rayuwa masu muhimmanci.


Onanuga ya bayyana hakan ne a ranar Talata cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, yayin da ake ci gaba da sukar yadda bashin kasar ke karuwa daga bangaren jama’a