Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da shanu 15 da kayan abinci ga fursunoni da ke cibiyoyin gyaran hali daban-daban a fadin jihar domin bikin babbar Sallah.


An bayar da tallafin ne ta hannun Shugabar Kwamiti ta Musamman na Jihar Kano, Hajiya Azumi Namadi-Bebeji, a ranar Talata a Kano.


Kayan abincin da aka bayar sun hada da shanu 15, buhunan shinkafa 115 masu nauyin kilo 50, jarkokin man girki manya guda 40 da sauran kayan girki 


Namadi-Bebeji ta ce wannan tallafin na sake tabbatar da kudirin gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na kula da jin dadin fursunoni da gyaren halayensu.


Ta kara da cewa gwamnatin jihar na ci gaba da jajircewa wajen tallafa wa marasa galihu da kuma inganta manufofin jin kai da ke da nufin dawo da martaba da mutuncin fursunonin da ke zaman gyaran hali.