Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya karɓi baƙuncin tsohon shugaban majalisar dattawa, Pius Anyim, a gidansa da ke Ikoyi a jihar Legas bayan nasarar da ya samu a zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa na jam’iyyar APC.


Jaridar Punch ta rawaito cewa Anyim, wanda shi ne shugaban kwamitin zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, ya kai ziyarar ne kwanaki biyu bayan bayyana Tinubu a matsayin ɗan takarar jam’iyyar a zaɓen shekarar 2027.


Kazalika Tinubu ya kuma gana da gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, da kuma gwamnan jihar Cross River, Bassey Otu.