Hukumar EFFC Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa a Nijeriya ta mika tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, zuwa Gidan Gyaran Hali na Kuje da ke Abuja domin fara zaman hukuncin daurin shekaru 75 da kotu ta yanke masa.


Hakan ya biyo bayan umarnin da Mai Shari’a James Omotosho na Babbar Kotun Tarayya da ke Maitama, Abuja, ya bayar a ranar Talata, bayan gabatar da Mamman a gaban kotun da EFCC ta yi.


DCL Hausa ta ruwaito cewa kotun ta kuma saurari bukatar EFCC na kwace wasu karin kadarori guda biyar da ake zargin suna da alaka da Mamman, ciki har da gidaje da otel-otel da ke Abuja da Kaduna.