Afuwar da shugaba Kais Saied ya yi masa na cikin shagulgulan sallar layya da ake gudanarwa a ƙasar a yau Laraba.


A watan Faburairu dai aka yankewa Saidani hukuncin zaman gidan yari na watanni 8, bayan da ya wallafa wani rubutu da yayi kan shugaban ƙasar a lokacin da ya ziyarci wani yankin da aka samu ambaliyan ruwa, inda ya bayyana shi a matsayin babban kwamandan duba gari.


Shi dai Saidani ya kasance ya kasance mai goyon bayan yadda gwamnatin Saied musamman yadda ta ke kulle ƴan adawa, sai dai a baya-bayan nan anga yadda shima ya ke sukar gwamnatin.