Gwamnan Jihar Oyo Seyi Makinde, ya tabbatarwa iyaye da al'ummar juharsa cewa Gwamnatinsa za ta yi duk mai yuwa wajen ganin ta kubutar da dukkan yara da malamai da aka yi garkuwa da su a ranar 16 ga watan Mayu a Karamar Hukumar Oriire, kuma za a dawo da su gida lafiya ga iyalansu.


Makinde ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a gidansa da ke Ikolaba yayin da yake karbar bakuncin mataimakinsa Bayo Lawal, da sauran masu mukaman gwamnati Musulmai a Jihar Oyo cikin shagulgulan salah