Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima ya sake jaddada kudirin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na rage wa ‘yan Najeriya radadin matsin tattalin arzikin da suke fuskanta.


Shettima ya bayar da wannan tabbacin ne a ranar Laraba yayin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan gudanar da sallar Eid-el-Kabir a filin Idi na Ramat Square da ke Maidugurin Jihar Brono 


Mataimakin Shugaban Kasar, wanda ya bayyana cewa tsadar rayuwa ta karu a duniya baki daya, ya roki ‘yan Najeriya da su ci gaba da hakuri da gwamnati.