Wani rahoto daga Hukumar Kula da ‘Yancin Addini ta Amurka (USCIRF) ya yi zargin cewa akwai kusan masu ɗauke da makamai 30,000 da ke gudanar da hare-hare a sassan Najeriya, lamarin da ke ƙara rura wutar rashin tsaro musamman a yankin Middle Belt da kudancin ƙasar.

Rahoton na watan Mayun 2026 mai taken “Masu Take ‘Yancin Addini da Ba na Gwamnati ba a Nijeriya: Mayaƙan Fulani” ya bayyana cewa mayaƙan na aiki ne cikin ƙananan ƙungiyoyi masu mutum tsakanin 10 zuwa 1,000.

A cewar rahoton, hare-haren da suke kaiwa sun yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane, da tarwatsa al’ummomi daga muhallansu, tare da ƙara tsananta rikice-rikicen addini a ƙasar.

Rahoton ya ce rikicin da mayaƙan ke haddasawa ya fi jawo asarar rayuka fiye da hare-haren ƙungiyoyin ‘yan tawaye da sauran masu aikata laifuka a shekarar da ta gabata.

USCIRF ta ce yawancin hare-haren na kai wa al’ummomin Kirista hari ne, duk da cewa Musulmai ma sun fuskanci kashe-kashe da sace-sace.

Rahoton ya kuma bayyana cewa wasu daga cikin ƙungiyoyin suna haɗa kai da ‘yanbindiga da kuma ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi.

Hukumar ta lura cewa mayaƙan kan kai hare-hare ne cikin dare, suna amfani da babura, bindigogi masu sarrafa kansu da adduna wajen kai farmaki kan ƙauyuka masu rauni.

A cewar rahoton, hare-haren sun raba fiye da mutum miliyan 1.3 da muhallansu a yankin Middle Belt, inda da dama ke rayuwa a sansanonin ‘yan gudun hijira cikin mawuyacin hali.