Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya umarci hukumomin tsaro da ma’aikatun da abin ya shafa da su ƙara ƙaimi wajen kare makarantu da ke yankunan da ake fuskantar barazanar tsaro a faɗin ƙasar nan.
Tinubu ya bayar da wannan umarni ne cikin saƙonsa na bikin Ranar Yara ta shekarar 2026 wato yau Laraba, kamar yadda jaridar PUNCH Online ta ruwaito.
Shugaba Tinubu ya ce gwamnati za ta ƙara ƙaimi wajen Samar da wani tsari na musamman na ceto yara da sauran al’umma masu rauni da aka yi garkuwa da su, musamman waɗanda aka sace a jihohin Oyo da Borno kwanan nan.
“A yayin da muke bikin wannan rana ta musamman, wadda ta zo daidai da bikin Idin babbar sallah, akwai wasu yara ‘yan Najeriya da malamansu a jihohin Oyo da Borno da ya kamata ace sun kasance tare da iyalansu, amma yanzu suna hannun masu garkuwa da mutane, cewar Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
“Ga waɗannan yaran da iyayensu da malamansu, zan fadi wannan a matsayina na uba kuma Shugabanku, ba a manta da ku ba, Ba a yi watsi da ku ba,” in ji Tinubu.
Shugaban ya bayyana cewa aya umurci dukkan hukumomin tsaro da abin ya shafa da su ci gaba tare da ƙara ƙaimi wajen gudanar da ayyukan ceto na sirri domin tabbatar da dawowar yaran da aka sace cikin ƙoshin lafiya.