Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Alhaji Atiku Abubakar ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC domin babban zaɓen shekarar 2027.
An sanar da sakamakon zaben ne a daren Laraba cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin X na jam’iyyar, inda aka bayyana cewa Atiku ya doke tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi da kuma tsohon ma’aikacin banki, Mohammed Hayatu-Deen a takarar.
Atiku ya kayar da Amaechi da Hayatudeen domin samun tikitin takarar shugaban ƙasa na ADC.
Sakamakon ƙarshe ya nuna cewa, Atiku Abubakar ya sami kuri’u 1,855,787 inda Amaechi ya samu kuri’u 509,397 sai kuma Hayatudeen kuri’u 180,903.
Jimillar kuri’un da aka kaɗa a zaɓen ya kama 2,546,457 inda Jimillar mambobin jam’iyyar da suka cancanci kaɗa ƙuri’a a zaɓen ya kai 3,113,599.
A karshe sanarwar ta taya murna ga Wazirin Adamawa Alhaji Atiku Abubakar.