Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu ya buƙaci al'ummar jihar da suka samu damar yin layya su raba nama ga mutanen da basu samu damar yin layyar ba kamar yadda Musulunci ya tanada.

Gwamnan ya yi wannan bayani ne a saƙonsa na ranar Idi a jiya Laraba. A cewarsa, yin hakan zai kawo “sauƙi ga mutane masu rauni, baya ga samun lada daga Allah”.

Ya ƙara da cewa Musulunci ya riga yayi bayani kan yadda ake raba naman layya, saboda haka ya kamata al'umma su bi ƙa'idar. A cewarsa, gwamnatin jihar na kashe maƙudan kuɗaɗe a kowace shekara wajen tallafa wa malaman addini da mabuƙata da ƴan-gudun hijira waɗanda rashin tsaro ya tarwatsa, da kuma marasa ƙarfi.

Sokoto, da ke Arewa-maso-Yammacin Najeriya, na cikin jihohin da rikicin ƴanbindiga ya tarwatsa mutane da dama, waɗanda suka bar muhallansu.

A jiya Laraba ne Musulmai a Najeriya da ma wasu ƙasashen duniya suka yi bikin sallar Idin layya, inda Musulunci ya buƙaci masu hali suyi yanka domin yin koyi da Annabi Ibrahim