Masu amfani da layukan sadarwa a Najeriya sun sake samun damar cin gajiyar ayyukan aron katin waya na gaggawa bayan Hukumar Kare Gasa da Kare Haƙƙin Mabukata ta Tarayya (FCCPC) ta dakatar da aiwatar da dokokinta na bayar da rancen kuɗi ta yanar gizo da hanyoyin zamani, wato ‘Digital, Electronic, Online or Non-Traditional Consumer Lending (DEON) Regulations 2025’.
Matakin ya biyo-bayan umarnin da Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta bayar, inda ta umurci hukumar da ta dakatar da aiwatar da sabbin dokokin har sai an kammala shari’ar da ke ƙalubalantar ikon FCCPC na sa-ido kan tsarin aron katin waya da kamfanonin sadarwa ke bayarwa.
Da yake tabbatar da ci gaban, shugaban Ƙungiyar Masu Samar da Sabis na Aikace-aikacen Wayar Sadarwa ta Najeriya (Wireless Application Service Providers Association of Nigeria), Ayo Stuffman, ya ce an riga an dawo da sabis ɗin a kan layukan kamfanonin Airtel Nigeria da Globacom.
Ana sa ran dawo da wannan sabis zai amfani miliyoyin masu amfani da wayoyin hannu da ke dogaro da aron kati domin sadarwa, da kuma gudanar da ƙananan sana’o’i. Rahotanni sun nuna cewa kasuwar aron katin waya a Najeriya na da kimar sama da naira biliyan 400 a duk shekara.
Tun farko dai, FCCPC ta yi yunƙurin sanya tsarin aron katin waya ƙarƙashin sabbin dokokin bayar da rance ta yanar gizo, tana mai cewa an samu dubban ƙorafe-ƙorafe daga masu amfani da sabis dangane da matsalolin sirri, da kuma wasu hanyoyin da ake zargin basu dace ba wajen karɓar bashi.