Akalla mutane 16 ne suka mutu yayin da wasu 58 suka jikkata sakamakon hare-haren Isra’ila a kudancin Lebanon, kamar yadda hukumomin lafiya na Lebanon suka bayyana, yayin da Isra’ila ke kara tsananta hare-harenta tare da bayar da umarnin kwashe jama’a da dama daga yankin.

Kamfanin dillancin labarai na gwamnatin Lebanon, wato National News Agency, ya rawaito a ranar Alhamis cewa mutum shida daga cikin wadanda suka mutu ‘yan gida daya ne.

 Rahoton ya ce sun mutu ne sakamakon harin jirgin yaki maras matuki na Isra’ila yayin da suke kokarin tserewa da asubahin kan babbar hanyar Adloun, wata muhimmiyar hanya da ke hada Sidon da Tyre.

Harin ya zo ne yayin da Isra’ila ta fadada hare-haren bama-bamai a fadin kudancin Lebanon, inda ta kai hare-hare kan unguwannin da hanyoyi da kuma kayayyakin more rayuwar fararen hula.

Rundunar sojin Lebanon ta ce daya daga cikin sojojinta ya mutu a wani harin Isra’ila a yankin Nabatieh, wanda shi ne sabon hari a jerin hare-haren da ake kai wa jami’an sojin kasar , Sauran sojoji ma sun mutu a kwanakin baya a hare-haren da aka kai a kudancin Lebanon da kuma kwarin Beqaa ta yamma.