Majalisar dattawan Najeriya ta ce aƙalla mutane dubu 1,639 ne suka mutu sanadiyyar rikicin zaɓe daga shekarar 1999 zuwa 2023 a faɗin ƙasar.


Dan majalisar Opeyemi Bamidele daga jihar Ekiti ne ya sanar da alƙaluman a matsayin wata babbar matsala ga ƙasa, wadda ya kamata a taka mata birki.


Yana mai cewa bai kamata ƴan Najeriya su riƙa rasa rayukansu ba sanadiyyar muradunsu na siyasa.


Sanatan na jihar Ekiti, ya yi wannan kira ne cikin saƙonsa na babbar sallah a jiya Laraba.


Bamidele ya ce binciken cibiyar da ke bibiyar rikice rikice, shi ne ya gano yadda aka rasa rayukan ɗimbin mutane daga 1999 zuwa 2023, saboda rikicin zaɓe.